<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Zo, Mu Kawo Kukanmu, Yesu Yana Jiranmu LW44</title>
<lyrics>[V1]
 1) Zo, mu kawo kukanmu, Yesu yana jiranmu,
 Shi da kansa ba ya ƙi, yana so ya riƙa ji.

[V2]
 2) Shi ne Sarkinmu babba, mu ba za mu rasa ba.
 Kome yawan roƙonmu, shi zai biya bukatarmu.

[V3]
 3) Ga ni nan mai zunubi, Almasihu, sai ka ji.
 Cikin ikon jininka, kau da kayan laifina.

[V4]
 4) Ina neman hutawa, zo, ka shigo zuciyata.
 Karƃi mulki, kai kaɗai, babu sarkina, sai kai.

[V5]
 5) Cikin duniyan nan yanzu, Yesu, kana bi da mu.
 In mun gama aikinka, sai ka kai mu gidanka.</lyrics>
<hymn_number>44</hymn_number>
</song>